Majalisar Dokokin Masar Ta Amince Da Kafa Dokar Ta Baci A Kasar
Majalisar dokokin kasar Masar ta amince da kafa doka ta baci a kasar na tsawon wattannin ukku bayan harin ta'addancin da aka kai kan wasu wuraren bauta na kiristoci a ranar lahadin da ta gabata.
Tashar television ta Rusia al-yau ta bayyana cewa majalisar dokokin kasar masar ta amince da kafa doka ta baci na watanni ukku a duk fadin kasar don shawo kan tabarbarewan harkokin tsaro a kasar, musamman bayan harin ta'addancin da aka kai kan wuraren bautan kiristoci a ranar Lahadin da ta gabata.
Tun ranar lahadin ne shugaban kasar ta Masar Abdul fatah Sisi ya bada sanarwan kafa doka ta bacin, amma majalisar dokokin ta tabbatar da ita ne zamanta na yau kamar yadda tsarin mulkin kasar ya bukata.
Mutane 45 ne suka rada rayukansu a wasu hare haren ta'addanci wanda wasu yan konan bakin wake suka kai a wani cuci a birnin Eskandaria na bakin ruwa da kuma garin Tanta a cikin kasar ta Masar.