Masar : An Daure Tsohon Minista Shekara 7 A Gidan Yari
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19454-masar_an_daure_tsohon_minista_shekara_7_a_gidan_yari
Wata Kotu a Masar ta yankewa tsohon ministan cikin gidan kasar, Habib al-Adly, hukuncin zamen gidan yari na shekara bakwai bisa samunsa da laifin cin hanci da rashawa.
(last modified 2018-08-22T06:59:58+00:00 )
Apr 15, 2017 10:12 UTC
  • Masar : An Daure Tsohon Minista Shekara 7 A Gidan Yari

Wata Kotu a Masar ta yankewa tsohon ministan cikin gidan kasar, Habib al-Adly, hukuncin zamen gidan yari na shekara bakwai bisa samunsa da laifin cin hanci da rashawa.

Wannan dai na daya daga cikin shari'ar da akeyi wa mayan jami'an tsohuwar gwamnatin Hosni Moubarak.

Mista al-Adly shi ne ya jagoranci hukumar 'yan sanda ta Masar a lokacin tsohon shugaba Mubarak kuma ana zarginsa da wuce gona da iri kan masu zanga-zanga lamarin da ya kasance tushen boren da ya kai ga hambarar da gwamnatin Husni Mubarak a shekara 2011.

A yayin zamen kotun na yau Asabar an kuma gurfanar da wasu jami'an ma'aikatar cikin gidan kasar da su ma ake zarginsu da karkata akalar wasu kudade da yawansu ya kai kimanin Miliyan 104 na Yiro Euro). 

Wannan hukuncin wanda Habib al-Adly na iya daukaka kara akansa na zuwa ne a kasa da wata guda bayan sakin Husni Mubarak wanda wata kotu ta wake shi daga tuhume-tuhumen kisan masu zanga-zanga a lokacin boren na waccen lokacin.