Masar Da Habasha Za Su Warware Takaddamar Da Ke Tsakaninsu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19638-masar_da_habasha_za_su_warware_takaddamar_da_ke_tsakaninsu
Mahukuntan masar da Habasha sun jadda cewa za su shawo kan matsalolin da ke tsakaninsu da suke da alaka da batun gina katafariyar madatsar ruwa ta al-nahdah da kasar ta Habasha ke yi, inda Masar ke ganin hakan a matsayin wata babbar matsala a gare ta.
(last modified 2018-08-22T06:59:59+00:00 )
Apr 20, 2017 13:17 UTC
  • Masar Da Habasha Za Su Warware Takaddamar Da Ke Tsakaninsu

Mahukuntan masar da Habasha sun jadda cewa za su shawo kan matsalolin da ke tsakaninsu da suke da alaka da batun gina katafariyar madatsar ruwa ta al-nahdah da kasar ta Habasha ke yi, inda Masar ke ganin hakan a matsayin wata babbar matsala a gare ta.

Kamfanin dilalncin labaran kasar Jamus ya bayar da rahoton cewa, shugaban kasar Masar Abdul Fattah Sisi ya tarbi ministan harkokin wajen kasar Habasha Workneh Gebeyehu a fadarsa da ke birnin Alkahira, inda suka tattauna muhimman batutuwa da suka jawo takun saka a tsakaninsu, da kuma yadda za a warware su ta hanyoyi na fahimtar juna.

Ministan harkokin wajen kasar Habasha Workneh Gebeyehu ya sheda wa manema labarai a birnin Alkahira cewa, ganawarsa da manyan jami'an gwamnatin Masar ta yi armashi matuka, kamar yadda bangaren gwamnatin kasar Masar su ma suka tabbatar da hakan.