-
Kotu Ta Ba Da Umurnin Tsare Tsohon Ministan Abuja A Gidan Yari
May 10, 2017 14:54Wata kotun tarayya a Abuja fadar mulkin Najeriya ta bayar da umarnin garkame tsohon ministan birnin tarayyar Abuja, Bala Muhammad a kurkuku.
-
An Nada Dan Najeriya Amaju Pinnick, Sabon Shugaban CAF
May 10, 2017 01:19Hukumar kwallon kafa ta Afrika ta nada shugaban hukumar kwallon kafa na Najeriya (NFF) Amaju Pinnick, a masatyin sabon shugaban kwamitin shirya wassanin kwallon kafa na Afrika cewa da (AFCON).
-
Najeriya: Shugaba Buhari Ya Sake Komawa London Domin Kula Da Lafiyarsa
May 08, 2017 03:01Shugaba Buhari na tarayyar Najeriya ya sake tafiya birnin London na kasar Birtaniya domin duba lafiyarsa.
-
Boko Haram Ta Saki Wasu Karin 'Yan Matan Chibok 82 Da Ta Yi Garkuwa Da Su
May 07, 2017 01:05Majiyar fadar shugaban Nigeriya ta sanar da cewa: Mayakan kungiyar Boko Haram sun saki wasu karin 'yan matan Chibok 82 da suka yi garkuwa da su tun a shekara ta 2014.
-
Rundunar Sojin Chadi Ta Tabbatar Da Kashe Sojojinta 9
May 06, 2017 12:48Rundinar sojin Chadi ta tabbatar a hukumance da kashe sojojinta tara da kuma jikkatar wasu 20 a yayin wani hari da 'yan ta'addan boko haram suka kai masu a garin Kaiga.
-
Mayakan Kungiyar Boko Haram Sun Kai Hari A Garin Kondoga Na Gabacin Jihar Borno
May 06, 2017 08:48Wasu majiyoyin tsaro a jihar Borno na tarayyar Nigeria sun bayyana cewa wasu yan kunan bakin wake biyu sun tarwatsa kansu a cikin mutane a jiya jumma a garin Konduga, wanda ya kai ga mutuwar mutane 5 fararen hula da kuma raunata wasu 6.
-
An Dage Ziyarar Da Shugaban Nijar Zai Kai Nijeriya Don Ganawa Da Buhari
May 05, 2017 05:16Fadar shugaban kasar Nijeriya ta sanar da soke ziyarar da a baya aka shirya shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou zai kai Nijeriya don ganawa da takwararsa na kasar Muhammadu Buhari har sai zuwa wani lokaci na gaba.
-
Sojoji Sun Hallaka 'Yan Kunar Bakin Wake 3 Dake Son Kai Hari Sansanin Soji A Maiduguri
May 04, 2017 06:53Sojojin Nijeriya sun hallaka wasu 'yan kunar bakin wake su uku da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne a daren jiya Laraba a lokacin da suka yi kokarin kai hari wani sansanin sojin a garin Maiduguri da ke jihar Borno.
-
Wata Kotu A Jigawa Ta Jefa Tsohon Gwamnan Jihar Sule Lamido Kurkuku
May 02, 2017 12:45Wata kotu a birnin Dutse na jihar Jagawa ta bukaci a ajiye tsohon gwamnan jihar Sule Lamino a gidan kaso kafin ta yi nazarin bukatar belinsa.
-
An Gurfanar Da Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido A Gaban Kotun
May 02, 2017 06:45Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, a gaban wata kotun majistire da ke garin Dutse, babban birnin jihar Jigawan, bisa wasu zargi guda hudu da suke masa da suka da kalaman tunzura mutane.