An Nada Dan Najeriya Amaju Pinnick, Sabon Shugaban CAF
Hukumar kwallon kafa ta Afrika ta nada shugaban hukumar kwallon kafa na Najeriya (NFF) Amaju Pinnick, a masatyin sabon shugaban kwamitin shirya wassanin kwallon kafa na Afrika cewa da (AFCON).
kamfanin dilancin labaren Afrika na APA wanda ya rawaito labarin ya ce Mista Pinnick ya maye gurbin tsohon shugaban hukumar CAF, Issa hayatu dan asalin kasar Kamaru.
Dama Mista Pinnick mamba ne a kwamitin shirya wassanin kwallon kafa na kasa da kasa a hukumar kwallon kafa ta duniya cewa da FIFA.
A yanzu Mista Pannick shi ne keda nauyin sanya akan wasanin kwallon kafa a kasashen da ke daukar bakuncin gasar.
A hannun daya kuma a nada dan kasar Ghana, Kwesi Nyantakyi mataimakin shugaban kwamitin na farko, yayin da aka nada dan kasar Congo, Constant Omari, a matsayin mataimaki na biyu.