Wata Kotu A Jigawa Ta Jefa Tsohon Gwamnan Jihar Sule Lamido Kurkuku
Wata kotu a birnin Dutse na jihar Jagawa ta bukaci a ajiye tsohon gwamnan jihar Sule Lamino a gidan kaso kafin ta yi nazarin bukatar belinsa.
Jaridar Daily Trust ta Nigeria ta bayyana cewa wani alkalin kotun majetrate ya bukaci a ajiye masa Alhaji Sule Lamido a gidan kaso har zuwa ranar 4 ga watan Mayu don ya sami damar nazarin belinsa.
A jiya ne dai jami'an tsaro suka kama Alhaji Sule Lamido a gidansa da ke Kano sannan suka binciki gidajensa da ke Kano da Dutste, sai kuma a safiyar yau suka zo da shi gaban kotu a birnin Dutse tare da tuhumar sa da laifuffuka guda ukku wadanda suka hada da tada hankalin jama'a, ingiza mutane don tada hankali da kuma laifin badda kama don aikata laifi wadanda suka sabawa sassa na 113, 114 da 117 na dokokin Penal cort.
Labarin ya kara da cewa yansanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa magoya bayan tsohon gwamnan kafin a kai shi gidan yari.
Alkalin koton Usman Mohammed Lamid, ya daga karar zuwa ranar Alhamis lokacinda zai ci gaba da sauraron karar sanan ya dubi yiyuwan bada belinsa.