Kotu Ta Ba Da Umurnin Tsare Tsohon Ministan Abuja A Gidan Yari
Wata kotun tarayya a Abuja fadar mulkin Najeriya ta bayar da umarnin garkame tsohon ministan birnin tarayyar Abuja, Bala Muhammad a kurkuku.
A zaman da kotun ta gudanar a yau a Abuja ta gabatar wa Bala Muhammad da wasu zarge-zarge da hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yi tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC take yi a kansa, wadanda suka shafi cin hanci da rashawa a lokacin da yake kan mulki a gwamnatin da ta gabata.
Bala Muhammad dai ya musunta zarge-zargen, tare da tabbatar da cewa ba shi da wani laifi a kan abin da ake tuhumarsa, da hakan ya hada har da karbar cin hanci na wasu kudade da suka kai Naira miliyan 550, da kuma kin bayyana kaddarorin da ya mallaka.
Alkalin kotun ya dage zaman shari'ar zuwa ranar 12 ga wannan wata na Mayu, inda ya bayar da umarnin a wuce da tsohon ministan zuwa gidan kurkukun Kuje.