-
Wasu Gungun 'Yan Bindiga Sun Farma Wani Ofishin 'Yan Sanda A Jihar Kogi Da Ke Tarayyar Nigeriya
Feb 11, 2017 02:50Wasu gungun mahara dauke da manyan makamai sun farma wani ofishin 'yan sanda a kauyen Eika da ke karamar hukumar Okehi a jihar Kogi a tarayyar Nigeriya, inda suka kashe mutane hudu kuma biyu daga cikinsu 'yan sanda.
-
An kashe Sojojijn Najeriya 7
Feb 10, 2017 12:40Kungiyar Boko Haram ta kashe Sojojin Najeriya 7 a arewacin kasar
-
JNI Da CAN Sun Yi Watsi Da Kiran Osinbajo Yayi Murabus, Sun Bukaci Addu'a Ga Buhari
Feb 10, 2017 02:10Manyan kungiyoyin musulmi da kirista a Nijeriya (wato Jama'atul Nasril Islam (JNI) da kuma Christian Association of Nigeria (CAN) sun yi kira ga illahirin magoya bayansu da su taya shugaban kasar Muhammad Buhari addu'ar samun sauki suna masu watsi da kiraye-kirayen da wasu suke yi ga mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo da yayi murabus.
-
Fiye Da Mutane 700 Ne Suka Gudanar Da Zanga Zanga Kan Tsadar Rayuwa A Birnin Abujan Nigeria
Feb 09, 2017 13:48Daruruwan mutane masu nuna rashin amincewarsu da yadda lamura suke tafiya a kasar da kuma mummunan halin da talaka yake ciki a kasar sun gudanar da zanga zanga a birnin Abuja babban birnin tarayyar Nigeria
-
Gwamnatin Jahar Lagos Ta Sake Dawo Da Batun Hana Saka Hijabi A Makarantu
Feb 08, 2017 16:53Gwamnatin jahar Lagos da ke tarayyar Najeriya ta sake dawo da batun hana dalibai mata a makarantun firamare da sakandare saka hijabi.
-
A Dai Dai Lokacinda Ake Tababa Kan Rashin Lafiyan Shugaban Nigeria Matamakinsa Ya Ce Yana Da Lafiya
Feb 07, 2017 02:49Mataimakin shugaban kasar Nigeria Prof Yemi Osingbanjo ya bayyana cewa shugaban kasar yana cikin koshin lafiya kuma zai dawo nan ba da dadewa ba.
-
Ana Zanga-zangar Nuna Rashin Amincewa Da Matsin Rayuwa A Nigeria
Feb 06, 2017 14:01Rahotanni daga Nijeriya sun bayyana cewar dubun dubatan 'yan kasar ne a biranen Abuja da Lagos suka gudanar da zanga-zangar lumana don nuna rashin amincewarsu da tsadar rayuwa da ake ciki da kiran gwamnati da ta yi wani abu, a daidai lokacin da wasu kuma suke gudanar da tasu zanga-zangar don nuna goyon bayan gwamnatin Muhammadu Buhari ta kasar.
-
Shugaba Buhari na Najeriya ya kara tsawaita hutunsa
Feb 05, 2017 14:15Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kara tsawaita lokacin hutunsa kamar yadda ya sanar da majalisa don ci gaba da samun magani a London a yayin da 'Yan Najeriya ke dakun isowarsa Abuja.
-
2Face Ya Soke Zanga-zangar Da Ya Shirya A Najeriya
Feb 05, 2017 07:14Sanannen mawakin nan na Najeriya 2Face ya ce ya jingine zanga-zangar da ya shirya jagoranata don nuna kyamar gwamnatin Muhamadu Buhari.
-
Obasanjo Ya Soki Masu Yada Jita-Jitan Mutuwar Shugaba Buhari
Feb 04, 2017 02:06Tsohon shugaban Nijeriya Chief Olesegun Obasanjo yayi kakkausar suka ga masu yada jita-jitan cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari ya rasu yana mai bayyana hakan a matsayin cin amanar kasa.