Ana Zanga-zangar Nuna Rashin Amincewa Da Matsin Rayuwa A Nigeria
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17385-ana_zanga_zangar_nuna_rashin_amincewa_da_matsin_rayuwa_a_nigeria
Rahotanni daga Nijeriya sun bayyana cewar dubun dubatan 'yan kasar ne a biranen Abuja da Lagos suka gudanar da zanga-zangar lumana don nuna rashin amincewarsu da tsadar rayuwa da ake ciki da kiran gwamnati da ta yi wani abu, a daidai lokacin da wasu kuma suke gudanar da tasu zanga-zangar don nuna goyon bayan gwamnatin Muhammadu Buhari ta kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:38+00:00 )
Feb 06, 2017 14:01 UTC
  • Ana Zanga-zangar Nuna Rashin Amincewa Da Matsin Rayuwa A Nigeria

Rahotanni daga Nijeriya sun bayyana cewar dubun dubatan 'yan kasar ne a biranen Abuja da Lagos suka gudanar da zanga-zangar lumana don nuna rashin amincewarsu da tsadar rayuwa da ake ciki da kiran gwamnati da ta yi wani abu, a daidai lokacin da wasu kuma suke gudanar da tasu zanga-zangar don nuna goyon bayan gwamnatin Muhammadu Buhari ta kasar.

Rahotannin sun ce mutane da dama ne suka fito a birnin Lagos da Abuja, babban birnin Tarayyar Nijeriya a yau Litinin don gudanar da zanga-zangar da abin da suka kira yanayin da gwamnatin Buharin take tafiyar da tattalin arzikin kasar lamarin da ya haifar da tsadar rayuwa da tsananin wahala ga al'ummar kasar.

Ita dai zanga-zangar ta yau wacce fitaccen mawakin kasar da aka fi sani da 2face ya kira, ta samu karbuwa a wajen wani adadi mai yawa na mutanen biranen biyu, duk kuwa da sanarwar da yayi na janye zanga-zangar.

A bangare guda kuma su ma wasu al'ummar kasar sun fito a wani bangare na birnin Abujan don nuna goyon bayansu ga shugaba Muhammadu Buhari da kuma yadda yake gudanar da mulkinsa musamman fada da rashawa da cin hancin da yake.

A wata sabuwa kuma, mataimakin shugaban Nijeriya Prof. Yemi Osinbajo, cikin wasu sakonni da ya buga a shafinsa na Twitter ya bayyana cewar gwamnatin ta su saurari kukan masu zanga-zangar yana mai cewa gwamnatin tana nan kan bakanta na ci gaba da gudanar da tsare-tsarenta wadanda take ganin idan har aka gudnar da su za su magance matsalolin da masu zanga-zangar suka tayar.