2Face Ya Soke Zanga-zangar Da Ya Shirya A Najeriya
Sanannen mawakin nan na Najeriya 2Face ya ce ya jingine zanga-zangar da ya shirya jagoranata don nuna kyamar gwamnatin Muhamadu Buhari.
Tun da farko dai mawakin ya shirya gudanar da zanga-zangar ne gobe Litinin a manyan biranen kasar Lagos da Abuja da kuma Kano, amma a sanarwar da ya aikewa jama’a yace ya soke gangamin saboda fargaban abin da zai biyo baya.
Shi dai mawakin mai suna Innocent Idibia da aka fi sani da 2Face ya nemi jama’a ne da su shiga zanga-zangar da ya shirya yi daga gobe Littini saboda a nuna rashin gamsuwa da matsanancin halin rayuwa da jama’a ke ciki.
Kafin hakan dai a ranar Alhamis rundunar ‘yan sandan kasar ta hana a yi zanga-zangar saboda rashin tabbas akan yadda zata kasance.