Shugaba Buhari na Najeriya ya kara tsawaita hutunsa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17361-shugaba_buhari_na_najeriya_ya_kara_tsawaita_hutunsa
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kara tsawaita lokacin hutunsa kamar yadda ya sanar da majalisa don ci gaba da samun magani a London a yayin da 'Yan Najeriya ke dakun isowarsa Abuja.
(last modified 2018-08-22T06:59:38+00:00 )
Feb 05, 2017 14:15 UTC
  • Shugaba Buhari na Najeriya ya kara tsawaita hutunsa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kara tsawaita lokacin hutunsa kamar yadda ya sanar da majalisa don ci gaba da samun magani a London a yayin da 'Yan Najeriya ke dakun isowarsa Abuja.

A cikin wata sanardaw da ya fitar a wannan Lahadi mai magana da yawun Shugaban Kasar ta Najeriya Femi Adeshina ya sanar da  cewa, shugaban Kasar Muhamadu Buhari ya sanar da Majalisa a rubuce a yau Lahadi kan bukatar tsawaita lokacin hutunsa domin samun damar kammala gwaje gwajen lafiyarsa da karbar sakamako.

A yau ne dai shugaban ya kamata ya dawo Abuja fadar gwamnatin Najeriya, Amma Sanarwar ta ce likitocin Buhari ne suka bukaci ya tsawaita hutun.

Sanarwar kuma ta ce shugaban ya mika godiyarsa ga ‘Yan Najeriya da ke masa add’o’I da fatan alheri.