-
Amurka Ta Kakaba Wa Wasu Jami'an Rasha 38 Takunkumi
Apr 06, 2018 17:35Ma'aikatar baitalmalin Amurka, ta sanar da kakaba wa wasu jami'an Rasha su 38 takunkumi, ciki har da wasu makusanta shugaban Rashar Vladimir Putin.
-
Rasha Ta Gargadi Birtaniya Da Cewa Tana Wasa Da Wuta Ne Kan Zargin Yunkurin Kisan Skripal
Apr 06, 2018 06:34A ranar jiya Alhamis ne dai kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya gudanar da wani zama na musamman, kan batun zargin da kasar Birtaniya take yi wa kasar Rasha na yunkurin kisan tsohon dan leken asirin Rasha Sergei Skripal, wanda ya koma kasar Birtaniya baki daya da rayuwa, a yayin zaman na jiya, jakadan kasar Rasha a majalisar dinkin duniya Vassily Nebenzia, ya gargadi kasar Birtaniya da cewa tana wasa da wuta ne a hannun kan shirya wannan wasan kwaikwayo.
-
Nato Ba Ta Son Yin Gasar Kera Makamai Da Kasar Rasha
Apr 05, 2018 06:28Babban magatakardar kungiyar yarjejeniyar tsaro ta "Nato" ne ya bayyana haka a jiya laraba a kasar Canada
-
Shuwagabannin Kasashen Iran, Turkiyya Da Rasha Na Taro Kan Siriya
Apr 04, 2018 11:18Yau Laraba, shuwagabannin kasashen Rasha da Turkiyya da kuma Iran, da wani taron a birnin Ankara na Turkiyya kan batun kasar Siriya.
-
Rasha Da China Suna Kara Karfafa Kawancensu A Bangaren Ayyukan Soji
Apr 04, 2018 05:49Wata babbar tawagar manyan hafsoshin sojin kasar China karkashin jagorancin ministan tsaron kasar ta China ta isa birnin Moscow na kasar Rasha.
-
Rasha : Gwamnan Kemerovo Ya Yi Murabus
Apr 01, 2018 10:31Gwamnan jihar Kemerovo, a Rasha ya yi murabus daga mukaminsa, mako guda bayan mummunar gobara data yi sanadin mutuwar mutane 64 a wani shagon sayar da kayayakin masarufi a yankin Siberiya.
-
Kasashen Iran, Turkiyya Da Rasha Zasu Yi Taro Kan Batun Siriya
Apr 01, 2018 09:56Kasashen Iran da Turkiyya da kuma Rasha, zasu yi wani taro domin tattauna wa kan batun Siriya.
-
Rasha Ta Kori Jami'an Diflomatsiyan Amurka 60
Mar 29, 2018 18:21Kasar Rasha ta kori jami'an diflomatsiyan Amurka guda 60, da kuma rufe karamin ofishin jakadancin Amurkar na birnin Saint-Pétersbourg, a mastayin maida martani kan korar nata jami'an da Amurkar ta yi biyo bayan zargin yunkurin kashe wani tsohon jami'in leken asirin Rashan da 'yarsa a Birtaniya.
-
Rasha Za Ta Mayar Da Martani Kan Korar Jami'anta na Diflomasiyya A Turai
Mar 27, 2018 17:23Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya bayyana cewa ko shakka babu Rasha za ta mayar da martanin da ya dace a kan korar jami'anta na diflomasiyya da wasu kasashen yammacin turai suka yi .
-
Ana Zaman Makoki A Rasha Domin Wadanda Gobara Ta Kashe
Mar 27, 2018 05:48An shiga zaman makoki na kwanaki uku a yankin Kemerovo, na kasar Rasha, bayan mumunnar gobara data yi ajalin mutum 64 a shekaran jiya Lahadi.