Ana Zaman Makoki A Rasha Domin Wadanda Gobara Ta Kashe
https://parstoday.ir/ha/news/world-i29398-ana_zaman_makoki_a_rasha_domin_wadanda_gobara_ta_kashe
An shiga zaman makoki na kwanaki uku a yankin Kemerovo, na kasar Rasha, bayan mumunnar gobara data yi ajalin mutum 64 a shekaran jiya Lahadi.
(last modified 2018-08-22T07:01:36+00:00 )
Mar 27, 2018 01:18 UTC
  • Ana Zaman Makoki A Rasha Domin Wadanda Gobara Ta Kashe

An shiga zaman makoki na kwanaki uku a yankin Kemerovo, na kasar Rasha, bayan mumunnar gobara data yi ajalin mutum 64 a shekaran jiya Lahadi.

Sanarwar da gwamnatin yankin na Kemerovo ta fitar, ta ce za a yi zaman makoki na tsawon kwanaki uku a yankin daga yau Talata, domin wadanda gobarar ta rutsa da su. 

Hukumomi a Rasha sun ce, gobarar da ta tashi a wani babban rukunin kantuna dake jihar Kemerovo, ta yi sanadin mutuwar mutane 64, da raunana mutane da kuma hadassa barna mai yawa.

Rasha na nan tana kokarin binciken musabbabin tashin gobarar, haka kuma ana kokarin gudanar da bincike kan irin wadannan rukunonin kantuna a duk fadin kasar, domin kiyaye gaba.

Da  yammacin shekaran jiya ne gobara ta tashi a rukunin kantuna mai bene hudu na birnin Kemerovo dake jihar Kemerovo na kasar, daga wurin wasan yara dake bene na hudu, inda wutar ta ruru zuwa sauran wasu wurare cikin sauri.