Rasha : Gwamnan Kemerovo Ya Yi Murabus
https://parstoday.ir/ha/news/world-i29544-rasha_gwamnan_kemerovo_ya_yi_murabus
Gwamnan jihar Kemerovo, a Rasha ya yi murabus daga mukaminsa, mako guda bayan mummunar gobara data yi sanadin mutuwar mutane 64 a wani shagon sayar da kayayakin masarufi a yankin Siberiya.
(last modified 2018-08-22T11:31:38+00:00 )
Apr 01, 2018 10:31 UTC
  • Rasha : Gwamnan Kemerovo Ya Yi Murabus

Gwamnan jihar Kemerovo, a Rasha ya yi murabus daga mukaminsa, mako guda bayan mummunar gobara data yi sanadin mutuwar mutane 64 a wani shagon sayar da kayayakin masarufi a yankin Siberiya.

Gwamna, Aman Touleïev, ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo na muntina uku da ofishinsa ya watsa, inda ya ce ya mika takardar murabus dinsa ga shugaban kasar Vladimir Putin.

M. Touleïev, dan shekara 73 dake rike da mukamin gwamnan yankin tun shekara 2007, ya ce ya yi hakan saboda murabus dinsa shi ne kawai zabi mai kyau, tuni kuma shugaban kasar Putin ya amunce da murabus din gwamnan. 

Iyalai da dama ne dai suka rasa 'ya yansu a gobara, lamarin da ya fusata 'yan kasar matuka.