Nato Ba Ta Son Yin Gasar Kera Makamai Da Kasar Rasha
(last modified Thu, 05 Apr 2018 06:28:45 GMT )
Apr 05, 2018 06:28 UTC
  • Nato Ba Ta Son Yin Gasar Kera Makamai Da Kasar Rasha

Babban magatakardar kungiyar yarjejeniyar tsaro ta "Nato" ne ya bayyana haka a jiya laraba a kasar Canada

Jens Stoltenberg, wanda ya gabatar da taron manema labaru na hadin guiwa da Fira ministan kasar Canada Justin Trudeau a birnin Ottawa ya ci gaba da cewa; Abin da kungiyar take son gani shi ne karfafa alaka mai amfani da Rasha ba sake komawa kan gasar kera makamai ba.

Bugu da kari Stoltenberg ya ce; A halin da ake ciki a yanzu kungiyar a shirye take ta bude tattaunawa da kasar Rasha.

Alaka a tsakanin Rasha da kasashen turai ta yi kamari a makwannin bayan nan  akan batun tsohon dan leken asirin Rasha Sergei Skripal da yammacin turai ke zargin Moscow da bai wa guba.

Da dama daga cikin kasashen turai sun kori jami'an diplomasiyyar kasar Rasha da kuma rage nasu jami'an da ke Moscow.

Rasha dai ta karyata zargin da ake yi ma ta.