-
Sojojin Siriya Sun Gano Makaman Amurka, Da Magungunan HKI A Yankin Qunaitra
Dec 23, 2018 19:24Sojojin kasar Siriya sun gano makamai kirar Amurka, da magunguna wadanda aka samar da su a HKI a yankin Qunaitra wanda ya dade yana hannun yan ta'adda.
-
Kasancewar Amurka A Siriya, Tun Farko Kuskure Ne_Iran
Dec 22, 2018 16:19Kwanaki kadan bayan da Shugaba Donald Trump na AMurka ya bayyana shirin janye sojojin kasarsa daga Siriya, Jamhuriya Musulinci ta Iran, ta bayyana hakan da cewa, tun farko dama kasancewar sojojin na Amurka a Siriyar kuskure ne.
-
Amurka Za Ta Janye Sojojinta Daga Siriya
Dec 20, 2018 10:39Shugaba Donald Trump na Amurka, ya ce kasarsa zata janye sojojinta kimanin 2,000 data jibge a arewacin kasar Siriya.
-
Amurka Za Ta Janye Ma'aikatan Diplomasiyyarta Daga Syria A Cikin Sa'o'i 24
Dec 20, 2018 06:58Kamfanin dillancin labarun Reuters ne ya ambato wani jami'in gwmanatin Amurka yana cewa kasar za ta janye dukkanin ma'aikatan harkokin waje daga Syria a cikin sa'o'i 24
-
Asad:Ana Bukatar Dala Billiyon 400 Don Sake Gina Kasar Siriya
Dec 14, 2018 11:53Shugaban kasar Siriya Bashar Al-asad ya kiyasta cewa ana bukatar tsakanin dalar Amurka billyon 250 Zuwa 400 don sake gina kasar bayan nasara da gwamnatinsa da kayawanta suka samu kan yan ta'adda.
-
Sojojin Siriya Sun Hallaka Wasu 'Yan Ta'adda 270 A Kudancin Kasar
Dec 03, 2018 16:19Kakakin sojin kasar Rasha a Siriya, Oleg Makarevich, ya bayyana cewar sojojin Siriya sun sami nasarar hallaka sama da 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Daesh su 270 a wasu hare-hare da suka kai lardin Suwayda da ke kudancin kasar Siriyan.
-
Amurka Ta Hallaka Wani Babban Jigon Kungiyar (IS) A Siriya
Dec 03, 2018 09:55Kawancen kasa da kasa da Amurka ke jagoranta kan yaki da mayakan dake ikirari da sunan jihadi a Siriya, ya sanar da hallaka wani babban jigo a kungiyar 'yan ta'adda ta (IS), wanda ke da hannu a kisan wani ma'aikacin agaji dan asalin Amurka mai suna Peter Kassig da kuma wasu fursunoni 'yan kasashen yamma da kungiyar ta yi garkuwa dasu.
-
Sojojin Siriya Sun Kakkabo Wasu Makamai Masu Linzami Na 'Isra'ila' Da Aka Harbo Su Cikin Kasar
Nov 30, 2018 11:15Sojojin Siriya sun kakkabo wasu makamai masu linzami na haramtacciyar kasar Isra'ila biyo bayan wasu hare-hare da suka kawo kudancin birnin Damaskus, babban birnin kasar Siriya lamarin da ya dakile kokarin wuce gona da irin da sahyoniyawan suka so yi.
-
Makaman Kariya Na Siriya Sun Maida Martani Kan Hare-haren Israi'la
Nov 30, 2018 04:43Makaman garkuwa na kare sararin samaniyar Siriya sun maida martani tare da kakkabo makamai masu linzami da jiragen sojin Isra'ila suka harba a kudancin birnin Damascos da kuma kudancin kasar.
-
Siriya : Rasha Ta Kai Wa 'Yan Ta'adda Hari Bayan Amfani Da Makamai Masu Guba
Nov 25, 2018 15:10Ma'aikatar tsaron Rasha ta sanar cewa jiragen sojinta sun kai jerin hare hare kan wasu sansanonin 'yan ta'adda a Aleppo, bayan da 'yan ta'addan suka kai hari da makamai masu guba a yankin.