Amurka Ta Hallaka Wani Babban Jigon Kungiyar (IS) A Siriya
Kawancen kasa da kasa da Amurka ke jagoranta kan yaki da mayakan dake ikirari da sunan jihadi a Siriya, ya sanar da hallaka wani babban jigo a kungiyar 'yan ta'adda ta (IS), wanda ke da hannu a kisan wani ma'aikacin agaji dan asalin Amurka mai suna Peter Kassig da kuma wasu fursunoni 'yan kasashen yamma da kungiyar ta yi garkuwa dasu.
An dai hallaka Abou al-Oumarayn ne a cikin hamadar Siriya dake zaman sansani na karshe na kungiyar ta (IS) ko kuma Da'esh.
Wata sanarwa da kakakin kawancen da Amurka ke jagoranta ya fitar dta ce nan gaba za'a fitar da cikakkun bayanai kan kisan babban dan ta'addan.
Abou al-Oumarayn an zarge shi da kisan Peter Kassig, t ahanyar yi masa yankan rago a watan Nuwamba na 2014, bayan sace shi a Siriya a cikin shekara 2013.