Asad:Ana Bukatar Dala Billiyon 400 Don Sake Gina Kasar Siriya
Shugaban kasar Siriya Bashar Al-asad ya kiyasta cewa ana bukatar tsakanin dalar Amurka billyon 250 Zuwa 400 don sake gina kasar bayan nasara da gwamnatinsa da kayawanta suka samu kan yan ta'adda.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto mataimakin Firai ministan kasar Yuri Borisv yana fadar haka bayan ganawarsa da shugaban kasar ta Siriya a jiya Alhamis a birnin Damascus.
Ofishin mataimakin Firai Ministan ya kara da cewa a ganawarsu na jiya bangarorin biyu sun tattauna batun makamashi, magunguna da kuma tada komatsar kamfanoni a kasar ta Siriya
Labarin ya kara da cewa a tattaunawan na jiyar, an yi maganar ruwan da gwamnatin kasar Rasha zata taka a shirin sake gina kasar bayan yaki, da kuma karfafa dangantakar siyasa tsakanin kasashen biyu.
Boriston ya ce akwai bukatar gwamnatin kasar Siriya ta gaggauta shirin farfado da tattalin arzikin kasar don kada yan ta'adda su yi amfani da talaucin da wasu yan kasar suke ciki don sake maidasu aikin daukar makama.