Amurka Za Ta Janye Sojojinta Daga Siriya
Shugaba Donald Trump na Amurka, ya ce kasarsa zata janye sojojinta kimanin 2,000 data jibge a arewacin kasar Siriya.
Shugaban ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter '' inda yake cewa mun murkushe kungiyar (IS) a kasar ta Siriya, yanzu lokaci ne da zarummanmu ya kamata su dawo gida.
Wanann dai ba shi ne karo na farko ba da shugaban yake bayyana anniyarsa ta janye dakarun na Amurka daga wannan kasa ta Siriya, saidai wannan karon shhugaban ya nuna da gaske yake kan wannan batun.
Tuni dai wasu jamia'n diflomatsiyya na Amurka dana ma'aikatar tsaron kasar ta Pentagone, suka fara nuna damuwa kan matakin, wanda suke ce zai kara baiwa gwamnatin Siriya da kawayenta Iran da Rasha karfi a kasar ta Siriya.