-
Nijar / Ta'addanci : An Rufe Wasu Kasuwanni Da Takaita Zirga-zirga Ababen Hawa
May 18, 2017 17:52Hukumomi a yankunan dake yammaci a Nijar sun sanar da fara aiki da wata doka data tanadi takaita zirga-zirga ababen hawa da kuma rufe wasu kasuwanni saboda barazanar yan ta'adda dake shigowa kasar daga Mali.
-
Harin IS Ya Kashe Mutane Sama Da 50 A Siriya
May 18, 2017 14:44Bayanai daga kungiyoyi masu zamen kansu na cewa mutane sama da 50 ne suka rasa rayukansu a wani hari da kungiyar 'yan ta'adda ta IS ta kai a wasu kauyuka biyu dake yankin Hama a tsakiyar kasar Siriya.
-
Jami'an Tsaron Iran Sun Dakile Wasu Kokari Na Kai Hare-Haren Ta'addanci A Kasar
May 13, 2017 19:14Ma'aikatar tsaro cikin gida da tattaro bayanan sirri na Iran ta sanar da nasarar da jami'an tsaron kasar suka samu wajen gano wasu makirce-makircen da aka kulla na kai hare-haren ta'addanci cikin kasar inda suka tarwatsa 'yan kungiyar da kuma kwace wasu ababen fashewa.
-
Harin IS Ya Hallaka Mutane 17 A Pakistan
May 12, 2017 14:38Rahotanni daga Pakistan na cewa a kalla mutane 17 ne suka rasa rayukansu kana wasu sama da 30 na daban suka raunana a wani harin kunar bakin wake da kungiyar 'yan ta'adda ta IS ta dauki alhakin kaiwa.
-
Bukatar Rasha Na Hadin Kan Kasashen Duniya Wajen Yakar Ayyukan Ta'addanci
May 10, 2017 05:56Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi kira ga kasashen duniya da su hada kai don yakar ayyukan ta'addanci a duniya, ya kuma bayyana cewa kasar Rasha a shirye take ta yi aiki da dukkan kasashen da suke da wannan manufar.
-
Amurka : Mai Yiwa Mun Hallaka Kwamandan IS Na Afganistan
Apr 29, 2017 11:04Ma'aikatar tsaron Amurka ta ce wata killah babban kwamandan kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh a Afganistan, Abdul Hasib ya hallaka a harin baya bayan nan data kai a gabashin kasar.
-
Taron Masanan Kasashen Yammacin Afirka Kan Fada Da Ta'addanci A Kasar Togo
Apr 28, 2017 05:54A ci gaba da kokarin samo hanyoyin da za a bi wajen fada da ta'addanci a kasashen Yammacin Afirka, masana harkokin tsaro daga kasashe 10 na Yammacin Afirka sun gudanar da wani taro a birnin Lome, babban birnin kasar Togo don tattauna hanyoyin da za a bi wajen fada da ta'addancin.
-
Taliban Ta Kashe Sojojin Afganistan 50
Apr 21, 2017 17:57Sojojin Afganistan 50 ne suka rasa rayukansu kana wasu a wani hari da kungiyar taliban ta dauki alhakin kai masu a wannan Juma'ar.
-
Wani Harin Bam Ya Kashe Mutane Akalla 43 A Syria
Apr 15, 2017 17:31Rahotanni daga Syria na cewa mutane akalla 43 ne suka rasa rayukansu a wani harin bam da aka kai da babbar mota kan wani ayarin motocin safa dake daukeda wasu mutanen da aka kwashe daga yankunan dake hannun gwamnati a wajen birnin Aleppo.
-
An Dakile Hari gabanin Bikin Ista A Pakistan
Apr 15, 2017 14:56Rundinar sojin Pakistan ta sanar da dakile wani hari da aka shirya kaiwa a jajibirin bikin Ista na mabiya Krista a wani samame data kai a yankin Lahore.