Harin IS Ya Kashe Mutane Sama Da 50 A Siriya
Bayanai daga kungiyoyi masu zamen kansu na cewa mutane sama da 50 ne suka rasa rayukansu a wani hari da kungiyar 'yan ta'adda ta IS ta kai a wasu kauyuka biyu dake yankin Hama a tsakiyar kasar Siriya.
Hukumar (OSDH) dake sa ido kan al'amuran kare hakkin bil adama a kasar ta Siriya ta ce mutane 52 ne wadanda suka da fararen hula 15 da mayakan dake goyan bayan gwamnati 27 da kuma wasu 10 da ba'a tantance su ba suka rasu a cikin harin.
Harin dai na kai shi ne a wannan Alhamis a kauyukan da suka hada da Aqareb na galibi yan Ismaili, da kuma Mabouje na galibi 'yan sunni da kuma tsiraru 'yan Ja'fari, Ismaili da kuma 'yan Alawuya.
Bayannan kuma sun ce da akwai wasu 'yan ta'adda na IS din 15 da suka hallaka a fafatawar da akayi a yankin.
Kamfanin dilancin labaren kasar ta Siriya (Sana) shi ma ya fitar da bayanai makamantan hakan, inda ya ce harin Aqareb ya yi sanadin mutuwar mutane 20 wadanda aka sassare, saidai ba tare da dauko batun waccen kauyen guda ba na Mabuje.