Wani Harin Bam Ya Kashe Mutane Akalla 43 A Syria
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i19458-wani_harin_bam_ya_kashe_mutane_akalla_43_a_syria
Rahotanni daga Syria na cewa mutane akalla 43 ne suka rasa rayukansu a wani harin bam da aka kai da babbar mota kan wani ayarin motocin safa dake daukeda wasu mutanen da aka kwashe daga yankunan dake hannun gwamnati a wajen birnin Aleppo.
(last modified 2018-08-22T06:59:58+00:00 )
Apr 15, 2017 13:01 UTC
  • Wani Harin Bam Ya Kashe Mutane Akalla 43 A Syria

Rahotanni daga Syria na cewa mutane akalla 43 ne suka rasa rayukansu a wani harin bam da aka kai da babbar mota kan wani ayarin motocin safa dake daukeda wasu mutanen da aka kwashe daga yankunan dake hannun gwamnati a wajen birnin Aleppo.

Hukumar kare hakkin bil adama ta OSDH a Syria wace ta rawaito labarin ta ce akwai mutane da dama da suka samu munanen raunuka, lamarion dake nuna cewa adadin mutanen da suka mutun zai iya karuwa.

wasu rahotanni na daban na cewa an koma aiwatar da shirin kwashe mutanen bayan wannan mumunan harin da har yanzu babu wata kungiya data dau alhakin kai shi.

A bisa yarjejeniyar da kasashen Qatar da Iran  suka cimma mutane kimanin 5,000 na yankunan Fuwa da Kafraya da 'yan tawayen na Syria suka mamaye yau kusa da shekara aka kwashe.

Ko baya ga hakan an kuma samu fitar da wasu mutanen kimanin 2,200 a yankunan Madaya da Zabadani dake karkashin ikon sojojin gwamnatin Syria a bisa wannan yarjejeniyar.