Harin IS Ya Hallaka Mutane 17 A Pakistan
(last modified Fri, 12 May 2017 14:38:36 GMT )
May 12, 2017 14:38 UTC
  • Harin IS Ya Hallaka Mutane 17 A Pakistan

Rahotanni daga Pakistan na cewa a kalla mutane 17 ne suka rasa rayukansu kana wasu sama da 30 na daban suka raunana a wani harin kunar bakin wake da kungiyar 'yan ta'adda ta IS ta dauki alhakin kaiwa.

Daga cikin wadanda suka jikkata a harin har da mataimakin shugaban majalisar datijan kasar Abdul Ghafoor Haideri da  da kuma wani babban jigo a jam'iyyar addini ta (JUI-F), Jamiat Ulema-e-Islam Fazl.

An nuno hoton bidiyon Haideri a wani gidan talabijin yana mai fadar cewa '' ina raye, Allah ya kubutar da ni', na jikkata aman ina da rai'' ya kara da cewa direba da wasu mutane dake zaune kusa da ni sun samu munanen raunuka. 

A sanarwar data fitar kungiyar IS ta ce wani dan kunar bakin wakenta ne ya kai harin.

An dai kai harin ne kan ayarin motocin tawagar jami'an dake kan hanyarsu ta  halartar wani taron yaye dalibai a lardin Mastung, dake gabashin Quetta a kudu maso yammacin kasar.