An Dakile Hari gabanin Bikin Ista A Pakistan
Rundinar sojin Pakistan ta sanar da dakile wani hari da aka shirya kaiwa a jajibirin bikin Ista na mabiya Krista a wani samame data kai a yankin Lahore.
Rundinar ta ce jami'an leken asirinta sun dakile wani mugun hari da ak shirya kaiwa a yayin bikin na gobe Lahadi a yankin na Lahore, ba tare da yin wani karin haske ba akan mutanen da aka kashe a samamen ba.
Saidai rundinar ta ce jami'an hudu sun jikkata a yayin samamen, aman sunyi nasara cafke wata mata da kuma wata riga da aka likawa boma-boma da kuma wasu abubuwa masu fashewa.
A yayin bikin Ista na shekara 2016 data gabata sama da mutane 70 ne da suka had ada yara da dama suka hallaka a wani harin kunnan bakin wake a wani wurin shan iska dake yankin na Lahore.
Kasar Pakistan dai na ci gaba da fuskantar barazana hare-haren ta'addanci inda ko a watan Fabrairu daya gabata mutane 130 ne suka gamu da ajalinsu, wanda kungiyar taliban ta ce iat keda alhakin kaisu.