-
Burundi : Majalisar Dokoki Ta Soki UNHRC Game Da Take Hakkin Dan Adam
Oct 03, 2017 07:23Majalisar dokokin kasar Burundi ta yi Allah wadai da shawarwarin da hukumar kare hakkin bil adama ta MDD (UNHRC) ta bayar, inda ta bada umarnin a sake kafa kwamitin da zai binciki laifukan take hakkin dan adam a kasar Burundin tun daga shekarar 2015.
-
Nijeriya Ta Bukaci ECOWAS Ta Dau Mataki Kan Kamaru Saboda Korar 'Yan Gudun Hijira
Sep 30, 2017 07:48Gwamnatin Nijeriya ta kirayi kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) da ta dau mataki kan kasar Kamaru saboda tilasta wa 'yan gudun hijira daga Nijeriya kimanin 4402 komawa gida cikin mawuyacin hali na musgunawa bayan sun gudu daga Nijeriya zuwa kasar ta Kamaru saboda hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram.
-
'Yan Adawan Kasar Togo Suna Ci Gaba Da Bukatar Shugaban Kasar Yayi Murabus
Sep 30, 2017 07:48Rahotanni daga kasar Togo sun bayyana cewar 'yan adawa a kasar sun ci gaba da gudanar da zanga-zangogi a wasu manyan biranen kasar a ci gaba da kiran da suke yi wa shugaban kasar Faure Gnassingbe da yayi murabus daga mukaminsa.
-
Nakiya Ta kashe Sojojin Kamaru Biyu
Sep 28, 2017 10:47Rahotanni daga Kamaru na cewa sojojin kasar biyu ne suka rasa rayukansu bayan da wata nakiya ta tarwatse a yankin arewa mai nisa na kasar.
-
Nijeriya : An Cafke Mutum 10 Bayan Zanga-zangar 'Yan Gudun Hijira
Sep 26, 2017 03:13Rahotanni daga Nijeriya na cewa an cafke mutane goma bayan zanga-zangar da 'yan gudun hijira boko haram suka yi a birnin Maiduguri dake arewa maso gabashin kasar.
-
Kotun Kolin Kenya Ta Bukaci A Binciki Hukumar Zabe
Sep 24, 2017 13:35Kotun kolin a Kanya ta bukaci da a binciki hukumar zaben kasar akan kura kuran da aka samu a babban zaben kasar da aka gudanar a watan Agustan da ya gabata.
-
Kasar Kamaru Ta Bukaci Kungiyoyin Kasa Da Kasa Da Su Yi Aiki Tare Da Nahiyar Afirka.
Sep 24, 2017 04:32Shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya yi ishara da mawuyacin halin da nahiyar Afirka take ciki, tare da tabbatar da cewa da akwai bukatar yin aiki tare da kungiyoyin kasa da kasa.
-
Gwamnatin Turkiya Ta Bude Sabbin Ofisoshin Jakadanci A Wasu Kasashen Afrika
Sep 22, 2017 00:31Gwamnatin kasar Turkiya ta bude wasu sabbin Ofisoshin jakadanci a wasu kasashen Afrika da zimmar fadada harkokin tattalin arziki da na siyasa da kasashen nahiyar
-
Morocco Zata Karbi Bakuncin Taro Kan sha'anin Tsaron Afrika
Sep 20, 2017 01:20Kasar Morocco za ta karbi bakuncin sabon taron dandalin Afrika game da batun tsaro tsakanin ranakun 8 zuwa 10 ga watan Oktoba mai zuwa.
-
Nijeriya : An Tsawaita Dokar Hana Fitar Dare A Jihar Abia
Sep 18, 2017 13:11Gwamnatin Jihar Abia a Najeriya ta sanar da tsawaira dokar hana fita da dare sakamakon rikicin da aka samu a wasu sassan kudu maso gabashin kasar tsakanin masu fafutukar kafa kasar Biafra da hausawa da kuma jami'an tsaro.