Burundi : Majalisar Dokoki Ta Soki UNHRC Game Da Take Hakkin Dan Adam
(last modified Tue, 03 Oct 2017 10:53:51 GMT )
Oct 03, 2017 10:53 UTC
  • Burundi : Majalisar Dokoki Ta Soki UNHRC Game Da Take Hakkin Dan Adam

Majalisar dokokin kasar Burundi ta yi Allah wadai da shawarwarin da hukumar kare hakkin bil adama ta MDD (UNHRC) ta bayar, inda ta bada umarnin a sake kafa kwamitin da zai binciki laifukan take hakkin dan adam a kasar Burundin tun daga shekarar 2015.

A makon jiya ne, hukumar UNHRC ta amince da wani kuduri inda ya tsawaita wa'adin hukumar bincike da shekara guda, don binciko laifukan take hakkin bil adama da aka aikata a kasar ta Burundi.

MDD ta nada masu bincike na UNHRC guda 3 a watan Satumba, inda ta gabatar da wani rahoto wanda ya nemi kotun hukunta laifukan yaki ta kasa da kasa ICC da ta bude tuhumar nan da ake zargin gwamnatin Burundi na take hakkin dan adam tun daga shekarar 2015.