Nijeriya : An Tsawaita Dokar Hana Fitar Dare A Jihar Abia
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i24149-nijeriya_an_tsawaita_dokar_hana_fitar_dare_a_jihar_abia
Gwamnatin Jihar Abia a Najeriya ta sanar da tsawaira dokar hana fita da dare sakamakon rikicin da aka samu a wasu sassan kudu maso gabashin kasar tsakanin masu fafutukar kafa kasar Biafra da hausawa da kuma jami'an tsaro.
(last modified 2018-08-22T07:00:43+00:00 )
Sep 18, 2017 13:11 UTC
  • Nijeriya : An Tsawaita Dokar Hana Fitar Dare A Jihar Abia

Gwamnatin Jihar Abia a Najeriya ta sanar da tsawaira dokar hana fita da dare sakamakon rikicin da aka samu a wasu sassan kudu maso gabashin kasar tsakanin masu fafutukar kafa kasar Biafra da hausawa da kuma jami'an tsaro.

Wata sanarwa da gwmanatin ta Abia ta fitar ta ce dokar hana fitar dare da aka ayyana a Aba babban birnin jihar daga karfe goma na dare har zuwa shida na safe an tsawaita shi da kwanaki goma daga yau Litini har zuwa ranar 28 ga watan nanna Satumba da muke ciki.

A ranar Lahadi data gabata ne dokar hana fitar ta kwanaki uku da aka kafa daga karfe shida na yamma har zuwa shida na safe ta zo karshe.

Sanarwar da kakakin gwaman jihar ta Abia, Enyinnaya Appolos, ya sanyawa hannu ta yaba da yadda aka samu dan sukuni a yankin.

Rikicin da aka shafe kusan mako guda ana yinsa a yankin ya dai yi sanadin mutuwar mutane da dama a yankunan da suka hada da Port Harcourt na jihar Rivers, Aba, da Asaba a jihar Delta.

A wani labari kuma wata babbar kotu da ke kudu maso gabashin kasar ta bayar da umarnin kai a kalla mutum 67 'yan kungiyar IPOB gidan yari, kan zarginsu da hannu a tashin hankali na fafatukar kafa kasar Biafra.