Nakiya Ta kashe Sojojin Kamaru Biyu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i24447-nakiya_ta_kashe_sojojin_kamaru_biyu
Rahotanni daga Kamaru na cewa sojojin kasar biyu ne suka rasa rayukansu bayan da wata nakiya ta tarwatse a yankin arewa mai nisa na kasar.
(last modified 2018-08-22T07:00:45+00:00 )
Sep 28, 2017 10:47 UTC
  • Nakiya Ta kashe Sojojin Kamaru Biyu

Rahotanni daga Kamaru na cewa sojojin kasar biyu ne suka rasa rayukansu bayan da wata nakiya ta tarwatse a yankin arewa mai nisa na kasar.

Kamfanin dilancin labaren AFP wanda ya rawaito labari, ya ce sojojin da suka rasa rayukansu na rundinar hadin gwiwar kasahen yankin ce ta yaki da kungiyar Boko Haram.

Lamarin dai ya auku ne da sanyin safiyar wannan Alhamis a lardin Bonderi dake shiyar arewa mai nisa a kusa da iyaka da tarayya Najeriya, a lokacin da motocin sojojin ke sintiri a yankin.

A shiyar arewa mai nisa na Kamaru dai ana danganta ire iren wadanan ayyukan da hare haren kunar bakin wake ga kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram.

Alkaluman da hukumomin Yaoude suka fitar sun nuna cewa tun daga shekara 2014 kimanin sojojin kasar 200 ne da kuma fararen hula 2,000 ne suka gamu da ajalinsu a yankin arewa mai nisa sakamakon ayyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram.