-
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Ta Mayar Da Martani Ga Kalaman Obasanjo
Jun 09, 2018 10:42Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta mayar da martani ga ikirarin tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo na cewa gwamnatin tana kokarin kitsa makarkashiyar kama shi, tana mai cewa mara gaskiya ne kawai zai ji tsoron shari'a.
-
Buhari Ya Sauya Ranar Dimokradiyya A Nijeriya Zuwa Ranar 12 Ga Watan Yuni
Jun 07, 2018 11:12Shugaban Muhamadu Buhari na Nijeriya ya sauya ranar dimokaradiyyar kasar daga 29 ga watan Mayu na kowace shekara zuwa ranar 12 ga watan Yuni don girmama zaben 12 ga watan Yunin shekarar 1993 da aka sanar da Cif Moshood Abiola a matsayin wanda ya lashe shi.
-
Wasu Gungun 'Yan Majalisa Najeriya Sun Nisanta Kansu Daga Sharuddan Da Majalisu Suka Kafa Wa Buhari
Jun 06, 2018 10:26Wasu gungun 'yan majalisar dattawa da ta wakilan Nijeriya sun nesanta kansu daga sharuddan da a jiya majalisar ta kafa wa shugaban kasar Muhammadu Buhari ko kuma su dau mataki kansa, suna masu jaddada goyon bayansu ga shugaban.
-
Buhari Ya Sa Wa Dokar Bai Wa Matasa Damar Tsayawa Takara Hannu
May 31, 2018 15:59Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya sanya hannu kan sabuwar dokar nan ta bai wa matasan kasar damar tsayawa takara a zabubbukan da za a gudanar a kasar; lamarin da matasan kasar suka jima suna jira.
-
Gwamnatin Najeriya Ta Sha Alwashin Sake Bayyana Sunayen Wadanda Ake Zargi Da Satar Kudin Gwamnati
Apr 15, 2018 17:24Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sake sanar da aniyarta ta sake fitar da sunayen wasu mutanen da take zargi da satar dukiyar gwamnatin kasar a shekarun baya lamarin da ya sanya tattalin arzikin kasar cikin tsaka mai wuya.
-
Buhari Yayi Karin Bayani Kan Dalilan Tsayawarsa Takarar 2019
Apr 11, 2018 17:32Shugaba Muhammadu Buhari yayi karin bayani dangane da dalilan sanar da tsayawarsa takarar shugabancin kasar a shekara ta 2019 bugu da kari kan batun rikicin makiyaya da manoma bugu da kari kan rikicin Boko Haram da 'yar makarantar Dapchi da 'yan Boko Haram din suke ci gaba da rike ta.
-
Shugaba Buhari Zai Fara Ziyarar Aiki Ta Kwanaki A Birtaniyya
Apr 09, 2018 11:07A wani lokaci a yau din nan Litinin ne shugaba Muhammadui Buhari na Nijeriya zai fara wata ziyarar aiki zuwa Birtaniya, don ganawa da jami'an kasar, shugabannin wasu kamfanonin mai bugu da kari kan halartar taron kasashen kungiyar renon Ingila ta Commonwealths.
-
Gwamnatin Kano Za Ta Kai Karar Buhari In Yaki Tsayawa Takara A 2019
Apr 07, 2018 11:20Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewar gwamnatinsa a shirye ta ke ta dau mataki na shari'a a kan shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari matukar ya ki amincewa ya tsaya takarar shugabancin kasar a shekara ta 2019.
-
Fadar Shugaban Nijeriya Ta Mayar Wa TY Danjuma Da Martani
Apr 01, 2018 05:07Fadar shugaban Nijeriya, a karon farko, ta mayar da martani ga kalaman tsohon shugaban sojojin kasar Laftanar Janar T.Y. Danjuma inda ya kirayi al'ummar kasar da su dau makami don kare kansu, tana mai bayyana wannan kalamai na sa a matsayin abin ban mamaki wanda ba abin da zai haifar in ban da karen tsaye ga doka da oda.
-
Osinbajo: Ba Za Mu Yi Shiru Kan Ta'annutin Gwamnatin Jonathan Ba
Mar 30, 2018 05:05Mataimakin shugaban kasar Nijeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewar ba za su yi shiru dangane da irin ta'annutin da gwamnatin Jonathan ta aikata ga tattalin arzikin Nijeriya din ba, yana mai cewa wajibi ne a ci gaba da sanar da 'yan Nijeriyan irin satar dukiyar kasa da aka yi a wancan lokacin wanda shi ne dalilin da ya sanya mutane cikin kuncin da suke ciki a halin yanzu.