Shugaba Buhari Zai Fara Ziyarar Aiki Ta Kwanaki A Birtaniyya
A wani lokaci a yau din nan Litinin ne shugaba Muhammadui Buhari na Nijeriya zai fara wata ziyarar aiki zuwa Birtaniya, don ganawa da jami'an kasar, shugabannin wasu kamfanonin mai bugu da kari kan halartar taron kasashen kungiyar renon Ingila ta Commonwealths.
Kakakin shugaba Buharin, Malam Garba Shehu ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwar da ya fitar a jiya Lahadi inda yace a yayin ziyarar shugaba Buharin zai gana da firayi ministar Birtaniyyan Theresa May, gabannin taron shugabannin kasashen kungiyar rainon Ingila - Commonwealth wanda za a gudanar daga ranar 18 ga watan Afrilu zuwa 20 ga watan.
Har ila yau sanarwar ta kara da cewa shugaba Buhari zai kuma gana da shugaban kamfanin mai na Royal Dutch Plc, Mista Ben van Beurden, da na kamfanin mai na Shell don tattaunawa kan batun batun zuba hannun jari na dala biliyan 15 a bangaren man fetur na Nijeriya din, wanda hakan zai taimaka wa tattalin arzikin Nijeriyan.
Har ila yau kuma Buharin zai gana da wasu manyan mutanen Birtaniyyan da 'yan Nijeriya bugu da kari kan ganawa da Archbishop na Canterbury, Justin Welby kan batun tattaunawa tsakanin addinai da kuma tabbatar da zaman lafiya a Nijeriya da kuma duniya baki daya.