Buhari Yayi Karin Bayani Kan Dalilan Tsayawarsa Takarar 2019
(last modified Wed, 11 Apr 2018 17:32:57 GMT )
Apr 11, 2018 17:32 UTC
  • Buhari Yayi Karin Bayani Kan Dalilan Tsayawarsa Takarar 2019

Shugaba Muhammadu Buhari yayi karin bayani dangane da dalilan sanar da tsayawarsa takarar shugabancin kasar a shekara ta 2019 bugu da kari kan batun rikicin makiyaya da manoma bugu da kari kan rikicin Boko Haram da 'yar makarantar Dapchi da 'yan Boko Haram din suke ci gaba da rike ta.

Shugaba Buharin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar bakuncin Archbishop na Canterbury, Justin Welby, a Abuja House da ke birnin London a ci gaba da ziyarar da yake yi a Birtaniyya, inda ya zargi wasu 'yan siyasa da hannu cikin rikicin makiyaya da manoma da ke faruwa a kasar inda yace duk da haka gwamnatinsa tana ci gaba da bin wasu hanyoyi don magance matsalar.

Shugaba Buhari ya ce matsalar makiyayya da manoma din wata tsohuwar matsala ce, to sai dai yanzu sakamakon yaduwar makamai a yankin Sahel da kuma 'yan bindiga dadin da a baya tsohuwar gwamnatin Libiya ta Mu'ammar Gaddafi ta horar da su yanzu kuma suka bazu bayan kashe shi, hakan ya kara sanya lamarin yayi kamari, yana mai cewa jami'an tsaron Nijeriyan sun sha kama irin wadannan mutane da kuma makaman.

Yayin da yake magana kan sanar da takararsa kuwa, shugaba Buhari ya ce, yayi hakan ne saboda ana ta maganganu kan ko zai tsaya ko ba zai tsaya ba, don haka ya ga lokaci ya yi ya kawo karshen maganar, don kuwa a cewarsa akwai abubuwa da yawa da ya kamata a yi da suka hada da batun tsaro, fada da rashawa da cin hanci, kyautata tattalin arziki, ayyukan noma da sauransu. Don haka bai kamata a bari wani abu ya kau da hankalin gwamnati daga wadannan abubuwan ba.

Dangane da Leah Sharibu, yarinya guda 'yar makarantan Dapchi da 'yan Boko Haram suke ci gaba da rike ta kowa saboda ta ki ta musulunta, shugaba Buhari ya ce suna ci gaba da bin lamarin ta hanyoyin da suka dace sannan kuma cikin sirri ba tare da yawan magana ba, wanda hakan ba zai taimaka ba, yana mai fatan ita ma nan ba da jimawa ba za a sako ta.