Fadar Shugaban Nijeriya Ta Mayar Wa TY Danjuma Da Martani
Fadar shugaban Nijeriya, a karon farko, ta mayar da martani ga kalaman tsohon shugaban sojojin kasar Laftanar Janar T.Y. Danjuma inda ya kirayi al'ummar kasar da su dau makami don kare kansu, tana mai bayyana wannan kalamai na sa a matsayin abin ban mamaki wanda ba abin da zai haifar in ban da karen tsaye ga doka da oda.
Fadar shugaban Nijeriya din ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Kakakin shugaban kasar, Malam Garba Shehu, ya fitar inda ya ce fadar shugaban kasar ta kadu ainun da wadannan maganganu wadanda za su karfafa masu laifi wajen yin karen tsaye ga halaltattun cibiyoyin gwamnati, yana mai cewa Nijeriya ba za ta ci gaba da wanzuwa ba matukar dai 'yan kasar za su dauki makami a kan halaltattun dakarun kasar.
Duk da cewa dai sanarwar ba ta ambaci sunan Janar Danjuman kai tsaye ba, amma dai sanarwar ta shawarci mutanen da ta kira, 'tsoffin shugabanni da su yi amfani da kafafen da suka cancanta wajen ba wa gwamnatin shawarwarin da suka dace ba tare da amfani da wasu kafafe wajen motsa hankulan al'umma ba.
A kwanakin baya ne dai Janar Danjuma, wanda ya taba rike mukamin babban hafsan hafsoshin sojojin Nijeriya din da kuma ministan tsaron kasar ya zargi sojojin Nijeriyan da hada baki da wasu 'yan bindiga wajen kashe mutane inda ya kirayi al'umma da su dau makami don kare kansu, lamarin da rundunar sojan Nijeriya din tayi Allah wadai da hakan da kuma cewa za ta dau mataki kan duk wanda aka same shi da daukar makami ba bisa ka'ida ba.