Pars Today
Shugaban kasar Chadi ya bada umurnin rufe ofishin jakadancin Amurka da ke birnin N'Djamena fadar mulkin kasar a matsayin maida martani kan umurnin shugaban kasar Amurka na sanya kasar Chadi cikin jerin kasashen da aka hana 'yan kasarta shiga cikin kasar Amurka.
Gwamnatin Chadi ta ce ta ji mamaki matuka da kuma rashin sanin dalilin sanya ta a cikin jerin kasashen da matakin shugaba Donald Trump na hana baki shiga Amurka ya shafa.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa, Amnesty international, ta zargi hukumomin kasar Chadi da mummunan take hakkin bil adama.
Kasar Faransa ta bukaci shugaba Idriss Deby na kasar Chadi da ya tsara zaben 'yan majalisar dokokin kasar.
Cibiyar watsa labarun kasar Libya ta Libyan Express ya nakalto jami'an kasar ta Libya suna cewa; An kashe mutane 9 a fadan da aka yi akan iyaka da Chadi.
Hukumomin Chadi sun yi bayyani kan rikicin diflomatsiyya na tsakaninsu da Qatar, wanda ya kai ga rufe ofishin jekadancin Qatar a Ndjamena.
A jiya laraba ne ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Chadi ta sanar da yanke huldar jakadanci da kasar Katar, tare da bai wa jami'an diplomasiyar kasar kwanaki 10 da su fice daga kasar.
A ci gaba da ran gadin da yake a wasu kasashen Afirka, shugaban kasar Masar Abdel Fattah Al-Sissi, ya gana da takwaransa na Chadi, Idriss Deby Itno jiya a birnin N’Djamena.
Ministan harakokin wajen kasar Tchadi ya bukaci kungiyoyin kasa da kasa da su dauki kwararen matakai game da kisan killar da ake yi a kasar Afirka ta tsakiya
Labaran da suke fitowa daga kasar Chadi sun nuna cewa jami'an tsaron kasar suna tsare da shugaban babbar jam'iyyar adawar kasar mai suna mohammad Adam.