An Kashe Mutane 9 Akan Iyakokin Libya Da Chadi.
(last modified Sat, 26 Aug 2017 18:59:36 GMT )
Aug 26, 2017 18:59 UTC
  • An Kashe Mutane 9 Akan Iyakokin Libya Da Chadi.

Cibiyar watsa labarun kasar Libya ta Libyan Express ya nakalto jami'an kasar ta Libya suna cewa; An kashe mutane 9 a fadan da aka yi akan iyaka da Chadi.

Majiyar ta ci gaba da cewa; Fadan ya barke ne a tsakanin wasu sojoji biyu da ke garin Al-kafrah, da kuma wasu 'yan kungiyar tawayen kasar Chadi. Sojojin Libya biyu ne suka mutu sai kuma 'yan tawayen kasar ta Chadi 7.

Garin al-Kafarah ne yana a cikin saharar Sirihanasiyah ne da ke tsakanin Libya da Chadi, wacce kuma take hadewa da iyakar kasar Sudan.

Pira ministan kasar Chadi, Albert Bahimi Badaki, ya ce kasarsa ta aike da jami'an tsaro zuwa yankin domin kalubalantar kai da komowar 'yan ta'adda.

Tun kifar da gwamnatin Mu'ammar Khaddafi a 2011 kasar Libya ta fada cikin  rashin tsaro.