Amnesty, Ta Zargi Gwamnatin Chadi Da Take Hakkin Bil Adama
(last modified Thu, 14 Sep 2017 15:43:25 GMT )
Sep 14, 2017 15:43 UTC
  • Amnesty, Ta Zargi Gwamnatin Chadi Da Take Hakkin Bil Adama

Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa, Amnesty international, ta zargi hukumomin kasar Chadi da mummunan take hakkin bil adama.

A rahoton data fitar yau Alhamis, kungiyar ta ce gwamnatin Chadi na amfani da wasu dokoki kuntatawa na jami'an leken asiri cikin gida wajen murkushe masu sukan ta karfin tsiya.

Kungiyar ta ce ta damu matuka akan koma baya da aka samu kan sha'anin kare hakkin bil adana a wannan kasa tun bayan sake zaben shugaba Idriss Deby a shekara 2016 data gabata, tare da kira ga kasashen yamma da su farka akan akan wannan lamari.

Rahoton dai ya karkata ne kan bayyanan da aka samu daga bangarorin 'yan adawa da kungiyoyin fara hula da kuma 'yan jarida.

Wannan dai na zuwa ne bayan da masu bayar da tallafi na kasashen ketare suka alkawarta baiwa kasar ta Chadi tallafi.

Haka zalika a kwanan nan ne kuma kasar Faransa ta bukaci shugaban kasar ta Chadi da ya shirya zaben 'yan majalisar dokokin kasar da gwmanatin kasar ta dage har zuwa wani lokaci da ba'a bayyana ba, saboda a cewarta dalili na rashin kudi.