Gwamnatin Chadi Ta Bada Umurnin Rufe Ofishin Jakadancin Amurka Da Ke Kasarta
(last modified Tue, 03 Oct 2017 19:00:36 GMT )
Oct 03, 2017 19:00 UTC
  • Gwamnatin Chadi Ta Bada Umurnin Rufe Ofishin Jakadancin Amurka Da Ke Kasarta

Shugaban kasar Chadi ya bada umurnin rufe ofishin jakadancin Amurka da ke birnin N'Djamena fadar mulkin kasar a matsayin maida martani kan umurnin shugaban kasar Amurka na sanya kasar Chadi cikin jerin kasashen da aka hana 'yan kasarta shiga cikin kasar Amurka.

Shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya sake yin dirar mikiya kan kasar Amurka tare da yin kakkausar suka kan matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na sanya sunan kasar Chadi cikin jerin kasashen da aka hana 'yan kasarta shiga cikin kasar Amurka, sannan ya bada umurnin rufe ofishin jakadancin Amurka da ke birnin N'Djamena a matsayin maida martani kan matakin na mahukuntan Amurka.

Har ila yau Shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya ki halattar zaman taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 72 da aka gudanar a birnin New York a matsayin nuna rashin amincewarsa da matakin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka kan kasarsa.

A ranar 25 ga watan Satumban da ya gabata ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sake rattaba hannu kan takardar bukatar hana al'ummun kasashen Koriya ta Arewa, Chadi, Iran, Libiya, Somaliya, Siriya da Venezuala takardar izinin shiga cikin kasar Amurka karkashin shirin yaki da ta'addanci.