Kasar Chadi Ta Yanke Huldar Jakadancinta Da Kasar Katar
Aug 24, 2017 09:18 UTC
A jiya laraba ne ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Chadi ta sanar da yanke huldar jakadanci da kasar Katar, tare da bai wa jami'an diplomasiyar kasar kwanaki 10 da su fice daga kasar.
Kasar Chadi tare da kasashen Senegal da Murtaniya sun shiga cikin wadanda suka kira yi jakadansu daga birnin Doha, bayan da Saudiyya ta jagoranci sauran kasashen larabawan tekun pasha yin fito fito na diplomasiyya da Katar.
Sai dai ita kasar Senegal ta mayar da jakadanta zuwa birnin Doha a shekaran jiya talata.
Saudiyya da Hadaddiyar Daular larbawa, Bahrai da Masar ne a gaba-gaba wajen yanke alakar diplomasiyya da Doha,bisa zarginta da su ke yi da taimakawa 'yan ta'adda da ta'addanci.
Tags