Pars Today
Masana tarihi sun bayyana cewa amincewa da gwagwarmayar da musulmi suka bayar a yakin duniya na farko, zai sa a magance matsalolin da ake fuskanta na tsawan shekaru kan kyammar Musulmi a wasu kasashen Turai.
Jirgin saman fasinjasa na kasar Indonesia dauke da mutane 189 ya yi hatsari a cikin teku.
Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Iran ya jaddada wajabcin hadin kan al'ummar musulmi musamman ganin yadda makiya addinin Musulunci suke ci gaba da kokarin raba kan al'ummar musulmi ta hanyoyi daban daban.
Kasashen Musulmi sun bukaci kafa wata rundinar kasa da kasa don kare yankunan Palasdinawa, bayan zubar da jinin Palasdinawa a zirin Gaza.
Musulmi 'yan Shi'a a duk fadin duniya sun fara gudanar da ranar Tasu'a don tunawa da rana ta tara na watan Muharram rana guda kafin faruwar Waki'ar Karbala inda Imam Husain (a.s) da iyalai da sahabbansa suka yi shahada a Karbala.
Al'ummar Afrika ta kudu na juyayin rasuwar daya daga cikin shugabannin yaki da mulkin wariyar launin fata na kasar Ahmed Kathrada wanda Allah ya yiwa rasuwa yana da shekaru 87 a duniya.
Asusun bayar da lamuni na duniya IMF ya amince da wasu daga cikin shawarwarin da bankin musulunci ya gabatar dangane da harkokin kudade a bankuna.
Ana ci gaba da yin Allawadai da kazamin harin da kawacen da Saudiyya ke jagoranta ya kai kan masu zamen makoki a birnin Sanaa na kasar Yemen inda mutane kimanin 140 suka rasa rayukansu, kana wasu 525 suka raunana.
Al'ummar Musulmi a kasahen duniya daban-daban na gudanar da bukukuwan babbar salla wace akafi sani da sallar layya, bayan da musulmai dake aikin hajji suka gudanar da hawan arfa a jiya Lahadi.
Yau Litinin ake bude taron koli na kungiyar kasashen larabawa karo na 27 a Nouakchott babban birnin kasar Mauritaniya.