Musulmi Na Bukukuwan Babbar Sallah
Al'ummar Musulmi a kasahen duniya daban-daban na gudanar da bukukuwan babbar salla wace akafi sani da sallar layya, bayan da musulmai dake aikin hajji suka gudanar da hawan arfa a jiya Lahadi.
Hakan kuma na zuwa a daidai lokacin da Alhazai ke gudanar da jifan shaidan a Mina, aikin da ke zaman cikamakin ayyyukan da aka wajabta yayin aikin hajji.
Aikin jifan shaidan na kasancewar daya daga cikin bangare aikin hajji mai wahala da hadari saboda cunkoson al'umma.
Idan ana tune a aikin hajjin shekarar da ta gabata, dubban alhazzai ne sukayi shahada sakamakon turmutsutsun da aka samu a lokacin jifan shaidan.
A kasashen Musulmi da dama inda za a ake gudanar da bukukuwan sallar ta layya, masu hali na yanka dabbobi musamman raguna sai kuma ziyartar 'yan uwa da abokan arziki.