An Manta Musulmin Da Suka Shiga Yakin Duniya Na Farko
(last modified Tue, 13 Nov 2018 06:19:19 GMT )
Nov 13, 2018 06:19 UTC
  • An Manta Musulmin Da Suka Shiga Yakin Duniya Na Farko

Masana tarihi sun bayyana cewa amincewa da gwagwarmayar da musulmi suka bayar a yakin duniya na farko, zai sa a magance matsalolin da ake fuskanta na tsawan shekaru kan kyammar Musulmi a wasu kasashen Turai.

Kungiyar ''The Muslim Experience'' wacce ta fitar da bayyanin ta ce musulmi sama da Miliyan hudu ne daga kasashe 19 na duniya aka dama dasu a lokacin yakin duniya na farko.

Saidai a cewar kungiyar har yanzu a cikin tarihi ba'a fayyace irin gumun muwar da musulmin suka bayar musamman a Biritaniya, da musulmi ke fuskantar kyamma daga wasu jam'iyyun siyasa.  

An kiyasta Indiyawa Miliyan 1,5 da suka shiga yakin duniya domin kare Biritaniya, 400,000 daga cikinsu musulmi ne, wanda kuma a cewar shugaban kungiyar ta ''The Muslim Experience'' Hayyan Bhabha an manta dasu a cikin tarihi, hatta wanda ake koyarwa a makarantun boko.

A kwanan nan ne dai aka cika shekara 100 da kawo karshen yakin duniya na farko 1914-1918.