Jirgin Saman Fasinja Ya Yi Hatsarin A Kasar Indonesia
Jirgin saman fasinjasa na kasar Indonesia dauke da mutane 189 ya yi hatsari a cikin teku.
Rahotani dake fitowa daga kasar Indenosia sun habarta cewa a safiyar wannan Litinin, da misalin karfe 6:30 na agogon kasar. wani Jirgin saman fasinja kirar Boeing 737 MAX da bai dade da fara aiki ba, ya bace bayan minti 13 da tashinsa daga filin jiragen sama da ke babban birnin kasar, in da ya fada cikin tekun Java.
Tuni dai jami'an agaji suka fara gudanar da bincike na kokarin neman jirgin , yayin da bayanai ke cewa, nutsewarsa ta kai mita 30-40 a cikin tekun.
Hukumar Kula da Sufuri ta kasar Indonesia ta ce, jirgin da ya tashi daga birnin Jakata na kan hanyarsa ne na zuwa birnin Pangkal Pinang, kuma a cikinsa fasinjoji 189 cikinsu akwai yaro guda da jarirai guda biyu. har ila yau daga cikin wadanda wannan ibtila'in ya ritsa da su akwai ma'aikatan ma'aikatar kudi ta kasar kimanin 20.
Rahotani sun bayyana cewa a ranar 15 ga watan Augusta na wannan shekara ta 2018 da muke ciki ne aka fara aiki da jirgin na kamfanin Lion Air.