Duniya Na Ci Gaba Da Allawadai Da Harin Saudiyya A Yemen
(last modified Mon, 10 Oct 2016 05:54:28 GMT )
Oct 10, 2016 05:54 UTC
  • Duniya Na Ci Gaba Da Allawadai Da Harin Saudiyya A Yemen

Ana ci gaba da yin Allawadai da kazamin harin da kawacen da Saudiyya ke jagoranta ya kai kan masu zamen makoki a birnin Sanaa na kasar Yemen inda mutane kimanin 140 suka rasa rayukansu, kana wasu 525 suka raunana.

Kasashen Amurka, Biritaniya, Iran, Siriya da kuma MDD wace ta bada alkalumen wadanda suka rasa rayukansu, sunyi tir da allawadarai da wannan harin.

Jamhuriya Musilinci ta Iran ta bakin ministan harkokin wajen ta Muhammad Javad Zarif tayi tir da kuma allawadai da harin tana mai danganta shi da ci gaba da cin zarafin bil adawa na Saudiyya a kasar ta Yemen. 

Amurka wace abokiyar huldar Saudiyya ce, ta ce ta kadu matuka dangane da wannan harin, kana ta ce zata sake nazari akan goyan bayan da take baiwa kawacen da Saudiyya ke jagoranta, bayan rage hakan a watanni baya.

A wata hira ta wayar tarho sakataren harkokin wajen Amurka John Kery, ya nuna matukar damuwarsa ga yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed ben Salmane tare da umurtarsa da daukan dukkan matakan da suka wajaba nan kada hakan ta sake aukuwa.