Taron Kungiyar Kasashen Larabawa Karo Na 27
(last modified Mon, 25 Jul 2016 06:46:33 GMT )
Jul 25, 2016 06:46 UTC
  • Taron Kungiyar Kasashen Larabawa Karo Na 27

Yau Litinin ake bude taron koli na kungiyar kasashen larabawa karo na 27 a Nouakchott babban birnin kasar Mauritaniya.

Taron na kwanaki biyu  zai maida hankali kan batutuwan da suka shafi tsaro a kasashen musamen a Libya, Iraki, Yemen, Syria, da kuma Palestine.

Hakazalika taron zai duba yiwuwar kafa wata rundina hadin gwiwa kasashen don yaki da ta'adanci. 

kasashen dai na fatan fitar da wata sanarwa ta bai daya a taron domin samun karin hadin kai a tsakaninsu.

Wanda shi ne karon farko da Mauritaniya zata karbi bakuncin taron kungiyar tun bayan zamen ta mamba a shekara 1973, kuma ana sa ran shugaban kasar ne Mohamed Ould Abdel Aziz zai jagoranci kungiyar na tsawan shekaru biyu masu zuwa.