Pars Today
A yau Litinin, shugaban Faransa Emmanuel Macron ke fara ziyarar kwanaki uku a China, in da ake sa ran zai kulla wata alaka ta musamman da gwamnatin kasar don yaki da ta’addanci da kuma magance matsalar dumamar yanayi a duniya.
Shugaban Kasar Faransa ya bukaci Sarkin Saudiya da ya kawo karshen killacewar da yake yi wa kasar Yemen.
A ranar Jumma'a 22 ga watan Disamban da muke ciki ne shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya kai ziyarar ba zata zuwa jumhuriyar Niger, inda ya gana da sojojin kasar ta Faransa da ke can, ya kuma gana da shugaban kasar ta Niger.
A yau Laraba ne mataimkain ministan harkokin wajen kasar Iran a bangaren sharia Abbas Araqchi zai fara tattaunawa karo na 4 tsakanin Faransa da Iran a birnin Paris.
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, ya fada cewa wajibi ne ya tattauna tare da shugaba Bashar al-Assad na Siriya domin kawo karshen yakin basasar kasar, da kuma shirya hanyoyin da za su tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a kasar.
Kasashen Jamus da Faransa tare da kasashen Afirka biyar na yankin Sahel sun gudanar da taro da nufin gaggauta fara aikin rundunar hadin gwiwa ta yaki da ta'addanci a yankin Sahel.
Kamfanin dillancin labarun faransa ya ce an kai harin ne jim kadan bayan da shugaban kasar Faransa ya fara ziyarar aiki a cikin kasar.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa zai fara wani ran gadi a wasu kasashen Afrika uku da suka hada da Bukina faso, Ivory Coast da kuma Ghana a wani mataki na karfafa alaka tsakanin Faransa da Afrika.
Shugaban kungiyar Tarayyar Afirka kuma shugaban kasar Guinea Conakry, Alpha Konde, ya bayyana cewar kasashen Turai suna da hannu cikin wani bangare na matsalolin da 'yan gudun hijira daga Afirka suke fuskanta a kasar Libiya.
Kasar Faransa ta ce za ta karbi kashin farko na bakin haure da reshen hukumar kula da kaurar bakin haure ta HCR a Nijar ya fitar dasu daga Libiya.