Macron Ya Bukaci Saudiya Da Ta Kawo Karshen Killace Kasar Yemen
Shugaban Kasar Faransa ya bukaci Sarkin Saudiya da ya kawo karshen killacewar da yake yi wa kasar Yemen.
Majiyar fadar Elize ta sanar da cewa a yayin zantawarsa da sarkin Saudiya Salaman bin Abdul-aziz ta hanyar tarho a wannan laraba, shugaban kasar Faransa Emaniel Macron ya bukaci sarki Salaman da ya kawo karshen killacewar da saudiya ke yi ga kasar Yemen,tare kuma da bayar da dama a shigar da kayen agaji gami da maguguna da al'ummar kasar cikin tsananin bukata.
Wannan firici na shugaba Macron na zuwa ne, yayin da kasar sa ke cikin sahun gaba wajen sayarwa Saudiya manyan makamai na zamani, wanda kuma hakan ke nuna cewa Faransa na da hanu wajen kisan gillar da ake yiwa al'ummar kasar yemen cikin yaki na shekaru uku.
Tun a 2015 ne dai sojojin na kasar Saudiyya suka fara kai hari akan kasar Yemen tare da cikakken goyon bayan Amurka, wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci fiye da rayuka 12,000 bisa kididdigar Majalisar Dinkin Duniya.