Libiya : Faransa Za Ta Karbi Bakin Hauren Farko Daga HCR
Nov 20, 2017 10:01 UTC
Kasar Faransa ta ce za ta karbi kashin farko na bakin haure da reshen hukumar kula da kaurar bakin haure ta HCR a Nijar ya fitar dasu daga Libiya.
Bakin hauren da suka isa a Yamai a ranar 11 ga watan Nuwamban nan, ana sa ran zasu isa Faransa kafin watan Janairu.
Kashin farkon dai wanda ya kunshi mata 15 d a yara hudu ya hada da 'yan Eritriya, Habasha da kuma Sudan dukkansu wadanda akayi tantance cewa suna cikin bukata ta kariya da kuma kula.
An dai kwaso ne daga kasar Libiya da ta kasa samun gindin zama tun bayan kifar da gwamnatin mirigayi Kanal Muammar Ghaddafi.
Tags