-
Macron Da May Sun Fuskanci Fushin 'Yan Majalisun Kasashensu Kan Harin Siriya
Apr 17, 2018 05:02'Yan majalisun kasashen Faransa da Birtaniyya sun tutsiye da kuma nuna fushinsu ga Emmanuel Macro, shugaban kasar Faransan da kuma Theresa May, firayi ministan Birtaniyyan sakamakon harin da suka kai kasar Siriya ba tare da izinin MDD ko kuma alal akalla izinin majalisun kasashen na su ba.
-
Amurka, Faransa Da Birtaniya Sun Kai Wa Siriya Hari
Apr 14, 2018 06:29Kasashen Amurka da Birtaniya da kuma Faransa, sun kai wa kasar Siriya harin soji a cikin daren jiya Juma'a wayewar safiyar wannan Asabar, kan abunda suka kira maida martani a kan shugaba Bashar Al'Asad na Siriya bisa zarginsa da amfani da makami mai guba a yankin Duma dake kusa da birnin Damascos a ranar 7 ga watan nan.
-
Siriya Ta Ce Hare-haren Da Aka kai Mata, Keta Dokokin Kasa Da Kasa Ne
Apr 14, 2018 06:28Gwamnatin Siriya ta danganta hare haren sojin da kasashen Amurka, Birtaniya da Faransa suka kai mata a cikin daren jiya da keta dokokin kasa da kasa da hurimin da kasar take da shi.
-
Skripal : Rasha Ba Za Ta Amince Da Duk Wani Rahoto Ba, Sai An Dama Da Ita
Apr 12, 2018 16:18Rasha ta yi watsi da rahoton da hukumar da ke yaki da yaduwar makami mai guba, ta fitar wanda ya tabbatar da zargin da Birtaniya ke yi na cewar Rashar ce ta kai harin da sinadarin da aka kera a kasar kan tsohon jami’in leken asirin Rashar Sergueï Skripal da 'yarsa.
-
Rasha Ta Ce Ita Ma Za Ta Kori Wasu Jami'an Diplomasiyyar Birtaniyya Daga Kasar
Mar 15, 2018 11:20Kasar Rasha ta ce nan ba da jimawa ba ita ma za ta kori wasu jami'an diplomasiyyar Birtaniyya da suke kasar a matsayin mayar da martani ga korar jami'an diplomasiyyarta su 23 da Birtaniyya ta yi biyo bayan rikicin da ya kunno kai tsakanin kasashen biyu dangane da batun amfani da gubar da aka yi a kan wani tsohon dan leken asirin Rashan a birnin London.
-
Rasha Ta Gargadi Birtaniya Kan Ta Guji Neman Yin Fito Na Fito Da Ita
Mar 15, 2018 05:39Ma'aikatar harkokin wajen kasar rasha ta sanar da cewa, Birtaniya ta zabi bin hanyar dagula lamurra a tsakaninta da Rasha, ta hanyar tuhumar Rasha da kashe tsohon jami'in leken asirinta.
-
Rasha Ta Ja Kunnen Birtaniyya Da Ta Sake Tunani Kafin Kawo Mata Harin Ta Yanar Gizo
Mar 14, 2018 11:06Kasar Rasha ta ja kunnen gwamnatin Birtaniyya da ta sake tunani sosai kafin ta aiwatar da barazanar kai mata hare-hare ta yanar gizo biyo bayan zargin da Birtaniyyan take yi wa Rashan na hannu cikin kokarin kisan gillan da aka yi wa wani tsohon dan leken asirin kasar a London a kwanakin baya ta hanyar amfani da guba.
-
Birtaniya: An Yake Hukunci A Kan Shugaban Kungiyar Masu Kiyayya Da Musulunci
Mar 09, 2018 05:01Wata kotun kasar Birtaniya ta yanke hukuncin dauri a gidan kaso a kan shugaban kungiyar Britain First mai adawa da addinin musulunci.
-
Kurdawa Na Tsare Da 'Yan Ta'addan Birtaniya Biyu A Siriya
Feb 09, 2018 15:48Myakan Kurdawa a Siriya sun ce suna tsare da wasu 'yan ta'addan kungiyar (IS) 'yan asalin kasar Birtaniya biyu, wadanda sanannu ne wajen azabtarwa da kuma hille kai.
-
Birtaniya : Boris Johnson Zai Fara Ziyara A Iran
Dec 09, 2017 05:54A wani lokaci a yau Asabar ne, ake sa ran ministan harkokin wajen kasar Birtaniya, Boris Johnson, zai fara wata ziyara a Iran.