Mar 09, 2018 05:01 UTC
  • Birtaniya: An Yake Hukunci A Kan Shugaban Kungiyar Masu Kiyayya Da Musulunci

Wata kotun kasar Birtaniya ta yanke hukuncin dauri a gidan kaso a kan shugaban kungiyar Britain First mai adawa da addinin musulunci.

Jaridar Yeni shafaq ta kasar Turkiya ta bayar da rahoton cewa, kotu yanke hukuncin daurin gidan kaso a kan Paul Golding shugaban kungiyar Britain First da mataimakiyarsa Jayda Fransen, bayan samun su da laifukan yada kiyayya a kan musulmi.

Rahoton ya kara da cewa, akalin kotun birnin Foxton na kasar Birtaniya Justin Barron, ya yanke hukuncin daurin makonni 18 a kan Golding, haka nan kuma makonni 36 a kan mataimakiyarsa Jayda Fransen.

Wannan hukunci ya zo ne sakamakon samun su da laifin yada kyamar musulmi tare da tunzura wasu domin cin zarafin musulmi da yin shishigi a kansu da kuma keta alfarmar wurarensu na ibada, da keta alfarmar mata masulmi musamman masu saka lullubi a kansu.

A kwanakin baya ne dai Donald Trump na Amurka, ya dauki wasu kalmomin kiyayya da musulunci daga shafin twitter na Jayda ya dora  akan shafinsa, lamarin da ya jawo masa gagarumar matsala, wanda ala tilas ya fito a tashar talabijin ta ITV ya nemi gafara.

Tags