Apr 12, 2018 16:18 UTC
  • Skripal : Rasha Ba Za Ta Amince Da Duk Wani Rahoto Ba, Sai An Dama Da Ita

Rasha ta yi watsi da rahoton da hukumar da ke yaki da yaduwar makami mai guba, ta fitar wanda ya tabbatar da zargin da Birtaniya ke yi na cewar Rashar ce ta kai harin da sinadarin da aka kera a kasar kan tsohon jami’in leken asirin Rashar Sergueï Skripal da 'yarsa.

Da take bayyana hakan yau Alhamis, a wani taron manema labarai, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Rashar, Maria Zakharova, ta ce Rasha ba za ta taba amunce wa ba da wani sakamakon bincike kan zargin muddin dai ba'a bawa kwararrunta ba damar shiga binciken.

Rashar dai na son a baiwa kwararunta damar bincikar sinadirin da aka hada wanda ake zargin anyi yunkurin kashe tsohon jami'in nata da shi a Biritaniya.

Yau Alhamis ne dai hukumar da ke yaki da yaduwar makami mai guba ta fitar da rahoton inda ta ce samfirin gubar da aka gudanar da bincike akai ya tabbatar musu da cewar sinadari ne na Navichok da aka yi amfani da shi, kuma Rasha ce ta sarrafa shi.

Rasha dai ta ce a shirye ta ke a koda yaushe don yin aiki tare, don warware wannan takaddama.

A halin da ake ciki dai Birtaniya ta bukaci gudanar da taron kwamitin Sulhu na MDD a mako mai zuwa, don tattauna rahoton hukumar da ke yaki da yaduwar makamai masu guba.

Tags