Apr 14, 2018 06:28 UTC
  • Siriya Ta Ce Hare-haren Da Aka kai Mata, Keta Dokokin Kasa Da Kasa Ne

Gwamnatin Siriya ta danganta hare haren sojin da kasashen Amurka, Birtaniya da Faransa suka kai mata a cikin daren jiya da keta dokokin kasa da kasa da hurimin da kasar take da shi.

Bayanai daga kasar ta Siriya sun ce hare haren sun shafi sansani soji da wuraren bincike na kimiya a kusa da birnin Damascos, da kuma wani binciken soji a kusa da birnin Homs.

Gidan talabijin din Siriya ya rawaito cewa, makaman kariya sararin samaniya na kasar sun maida martani kan hare haren kasashen uku, inda a birnin Homs suka yi nasara kakkabo makamai masu linzami.

Kamfanin dilancin labaren kasar na Sana, ya ce hare haren sojin na kasashen Amurka, Birtaniya da Faransa ba zasu kai labari ba.

Har zuwa lokacin Fasara wadanan labaren babu karin bayyani daga gwamnatin ta Siriya, akan irin barna ko hasara rayuka biyo bayan hare haren. 

Gwamnatin Siriya dai na mai musunta hannunta a cikin harin makami mai guda da aka zargin an kai a birnin Duma a ranar 7 ga watan nan, hasali ma a cewarta shiri ne kawai. 

Tags